Isa ga babban shafi
UN

Majalisar Dinkin Duniya Za Ta Kawar Da Fatara Cikin Shekaru 15

Paparoma Francis ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya, MDD inda ya yi marhabin da tsarin  da shugabannin kasashen duniya suka fitar don kawar da fatara a kasashen duniya nan da shekaru 15 masu zuwa.

Paparoma Francis na magana a zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke New York
Paparoma Francis na magana a zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke New York Reuters/路透社
Talla

Paparoma Francis wanda yake jawabi a zauren majalisar dake New York ya ce wannan na nuna cewa akwai alamun nasara nan gaba, kodashike tun ba'a kai koina ba wasu dake kushe shirin na ganin zance ne kawai.

Karkashin sabon tsarin akwai bukatu 17 da suka shafi ayyuka 169 domin kaiga kawar da fatara a fadin duniya, da samar da wadataccen kiwon lafiya, ilmi da magance dumamar yanayi, wanda zai ci kudi Dollan Amirka kusan triliyan biyar, duk shekara har zuwa shekara ta 2030, wato shekaru 15 masu zuwa.

Sabon tsarin zai maye gulbin maradun karni da ake kawo karshen sa wannan shekaran.
Babban Sakataren MDD Ban Kimoon ya bayyana sabon tsarin a matsayin ayyukan da za'ayi wa jama'a da duniya, kuma ana bukatar goyon bayan kowa.

Taron na kwanaki uku da aka fara yau, ana sa ran wasu shugabannin kasashen duniya suyi Magana gameda tsarin su don kaiga nasarar kawar da fatara a kasashen su.

Ciki akwai Shugaban Gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel, Fira Ministan India Narendra Modi da kuma Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.