Isa ga babban shafi
Forbes

Putin na Rasha ya fi Obama karfin fada a ji- Forbes

Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun dare shugaban Amurka Barack Obama a jerin sunayen masu karfin fada a ji a duniya da mujallar Forbes ta wallafa a bana.

Shugaba Obama na Amurka da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin.
Shugaba Obama na Amurka da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Wannan ne karo na bakwai da mujallar Forbes ta fara fitar da jerin matsayin sunayen masu karfin fada a ji a duniya.

Shugaban Rasha Vladimir Putin shi ne mai karfin fada aji a duniya a jerin ajin matsayin na mujallar Forbes.

Putin ya sake zarce Obama wanda ke dab da kawo karshen wa’adin mulkinsa a Amurka.

mujallar ta ce  Putuin na cikin manyan shugabannin duniya da ke yin yadda suka ga dama musamman yadda ya tunkari kasashen yammaci kan rikicin Ukraine da kuma rawar da Rasha ke taka wa a rikicin Syria.

Mujallar ta ce karfin fada a ji na Obama ya fadi inda ta bashi maki kasa da 50 saboda sai ya yi fadi-tashi kafin ya fadi a aji.

Mujallar ta ce Putin ya rage wa Amurka karfi da kuma kungiyar tsaro ta NATO

Shugabar gwamnatin Jamus Angel Merkel ce mujallar ta sanya a matsayi na biyu inda ta maye gurbin shugaba Obama na Amurka wanda yanzu ya koma matsayi na uku.

Fafaroma Francis ne a matsayi na hudu sai shugaban China Xi jinping a matsayi na 5

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.