Isa ga babban shafi
Vatican

Kiristoci na bikin Kirsimeti a fadin duniya

Yau 25 ga watan Disemba mabiya addinin Kirista a sassan duniya ke gudanar da bikin Kirsimeti domin murnar tunawa da haihuwar Yesu da suke bautawa.

Pope Francis ya bukaci Kiristoci su gujewa rayuwa mai tsada
Pope Francis ya bukaci Kiristoci su gujewa rayuwa mai tsada REUTERS
Talla

A daren jiya jajibirin Kirsmetin an yi wasan wuta a manyan biranen kasashen duniya domin murnar zagayowar wannan rana.

A jawabinsa a jajibirin Kirsemeti Shugaban Darikar Katolika Fafaroma Francis ya bukaci mabiya su rungumi rayuwa mai sauki, ba ta neman mallakar abin duniya ba.

Idan an jima a yau Juma’a Fafaroma zai gabatar da jawabin sakonsa na Kirismeti ga dimbin mabiya darikar katolika a filin st Peters a fadar Vatican.

Ana sa ran Fafaroma ya yi kira ga sasantawa da juna musamman a kasashen da ke fama da rikici.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.