Isa ga babban shafi
Faransa-ISIS

Ministocin tsaron kasashe sun lashi takobin murkushe IS

Ministocin tsaron kasashe 7 da ke yaki da Kungiyar IS sun lashi takobin karfafa rundunoninsu domin kawo karshan mayakan Jihadi musamman a cibiyoyin su dake Syria da Iraki.

Ministocin tsaron kasashe 7 da ke Yaki da IS a Iraqi da Syria
Ministocin tsaron kasashe 7 da ke Yaki da IS a Iraqi da Syria REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Ministocin sun sanar da haka ne bayan kammala taron bijiro da sabbin dabarun dakile IS baki daya a duniya.

A cewar Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter a yanzu Manufarsu ta farko ita ce kakabe IS baki daya a Syria da Iraki musamman manyan cibiyoyin mayakan da ke Raqa da Mosul.

Kana sai kuma a tabbatar da cewa babu IS a kowacce kusurwa da ke fadin duniya.

An gudanar da Taron na birnin Paris ba tare da halarci Rasha ba, da aka ce tana marawa shugaban Syria Bashar al-Assad baya.

Jagororin taron wato Faransa da Amurka bukatar su ita ce Rasha ta daina kai harin bama-bamai kan ‘yan adawar Syria da ke yaki da IS.

Sai dai kuma a ganawar da Ministan harkokin wajen Rashan Sergei Lavrov ya yi da takwaransa na Amurka a birnin Zurich John Kerry, ya ce nan bada jimawa ba za a fara tattaunawar samar da zaman lafiya a Syria.

Amma shi Ashton Carter na gani cewa babu amfani hada kai da Rasha kan lamarin Syria, domin kasa ce da ke karya dokoki da bin hanyoyin da basu da ce ba.

Taron na Paris dai ya samu halarcin Ministocin tsaron kasashen Amurka, Britaniya da Faransa da Jamus sai kuma Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.