Isa ga babban shafi
Girka-Turkiya

Tusk zai ziyarci Girka da Turkiya saboda masu hijira

Shugaban kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk, zai kai ziyara kasashen Girka da Turkiya yayin da ya ke kokarin samar da bakin zaren warware matsalar kwararar ‘yan gudun hijira.

Shugaban hukumar tarayyar Turai Donald Tusk.
Shugaban hukumar tarayyar Turai Donald Tusk. AFP / LOUISA GOULIAMAKI
Talla

Mr. Tusk ya ce, rage yawan ‘yan gudun hijirar da ke isa tsibirin Girka ta kasar Turkiya, shi ne babban matakin magance matsalar.

Yanzu haka sama da ‘yan gudun hijira dubu 25 ke zaune kara zube a Girka yayin da aka karfafa matakan tsaro a kan iyakar kasar.

Ana sa ran mahukuntan Birtaniya da Faransa za su tattauna a kan batun ’yan gudun hijra a wani taro da za su yi a yau Alhamis.

Firaministan Birtaniya, David Cameron da shugaban kasar Faransa, Francois Hollande za su gana a birnin Amiens na Faransa, inda za su zanta kan ta’addanci da rikicin kasashen Libya da Syria.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.