Isa ga babban shafi
Amurka

'Yan takarar Republican sun caccaki Trump

‘Yan takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Republican, Marco Rubio da Ted Cruz sun caccaki babban abokin hamayarsu Donald Trump a wata muhawara da ta gudana tsakaninsu a birnin Detroit da ke Michigan.

'Yan takarar Republican Marco Rubio da Donald Trump da kuma Ted Cruz.
'Yan takarar Republican Marco Rubio da Donald Trump da kuma Ted Cruz. REUTERS/Mike Stone
Talla

A yayin muhawar ta ranar Alhamis, Sanata Rubio daga jihar Florida ya caccaki Trump tare da jefa masa tambaya kan dalilin da ya hana shi maido da kamfanoninsa na kere tufafi Amurka daga kasashen China da Mexico, lura da ikirarin da Trump ke yi na cewa zai samar da ayyukan yi tsakanin al’ummar Amurka.

A martanin da ya mayar, Trump ya ce, Rubio na yawaita yi masa karya, yayin da ya ce, tuni ya fara shirin maido da kamfanonin daga kasashen na waje.

To sai dai Rubio ya jajirce kan cewa, Mr. Trump ba zai iya yin haka ba saboda ya fi samun riba a China da Mexico .

A na shi bangaren, Sanata Cruz daga jihar Texas ya bayyana Mr. Trump a matsayin dan takarar da bai dace ya kalubalanci Hillary Clinton ba ta jam’iyyar Democrat, tunda ya taimaka mata da kudi a can baya.

To sai dai Trump ya mayar masa da martani, inda ya ce, harka ce ta shiga tsakanisa da Clinton.

Tuni dai wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar Republican suka bukaci magoya bayan jam'iyyar da su yi watsi da Trump sakamakon abinda suka kira miyagun kalamansa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.