Isa ga babban shafi
Boko Haram

Boko Haram na rike da yankuna a Najeriya- Amurka

Babban kwamandan rundunar sojin Amurka da ke kula da sha’anin tsaro a Afrika, Janar David Rodriguez ya bayyana cewa, har yanzu akwai wasu yankunan arewacin Najeriya da ke hannun kungiyar Boko Haram.

Babban kwamandan rundunar Amurka da ke kula da sha'anin tsaro a Afrika, Janar David Rodriguez
Babban kwamandan rundunar Amurka da ke kula da sha'anin tsaro a Afrika, Janar David Rodriguez AFP PHOTO/Mandel Ngan
Talla

Mr.Rodriguez ya fadi haka ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi a gaban kwamitin majalisar dattawan Amurka da ke kula da sha’anin sojojin kasar, bayan kwamitin ya tambaye shi game da kungiyoyin Boko Haram a Najeriya da kuma Al-Shebab a Somalia.

Kalaman Janar Rodriguez na a matsayin kalubale ga hukumomin Najeriya wadda ta shafe shekaru bakwai tana fama da rikicin Boko Haram da ya lakume kimanin rayukan mutane dubu 20 tare da raba mutane sama da miliyan 2 da muhallansu.

Wannan dai na zuwa ne kusan watanni biyu da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya shaida wa sakatare Janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon cewa, babu wani yanki da mayakan Boko Haram ke rike da shi a Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.