Isa ga babban shafi
Turkiyya

Kungiyar TAK ta dauki alhakin harin Ankara

Kungiyar ‘yan tawaye ta kurdawa da ake kira TAK ta dauki alhakin harin ta’addancin da aka kaddamar a babban birnin Ankara na kasar Turkiyya a ranar Lahadin da ta gabata.

An dai yi amfani da mota ce makare da bama bamai a harin na ranar Lahadi a birnin na Ankara.
An dai yi amfani da mota ce makare da bama bamai a harin na ranar Lahadi a birnin na Ankara. EROL UCEM / AFP
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin Internet, kungiyar ta ce harin wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 37, na a matsayin martani ga aikin sojin kasar a yankin kudo maso gabashin kasar, inda kurdawa ke da yawa.

Kungiyar ta kara da cewa, ta kaddamar da harin ne da nufin kashe jami’an tsaro amma ba fararen hula ba.

Hukumomin Turkiyya dai sun dora laifin harin akan kungiyar PKK.

An dai yi amfani da mota ce makare da bama bamai a harin na ranar Lahadi wanda aka kai a wani yanki mai cike da hada hadar kasuwanci a tsakiyarAnkara.

Har yanzu dai akwai jama’a da dama da ke kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka samu a harin.

Ko a baya bayan nan, kungiyar TAK ta yi ikirarin cewa, ita ta kai harin da ya kashe mutane 29 a watan jiya a Ankara.

A bangare guda, kasar Jamus ta rufe ofishin jakadancinta da ke Ankara da kuma wata makarantarta da ke birnin Instanbul saboda fargabar hare haren ta’addanci.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.