Isa ga babban shafi
Brazil

Rousseff ta bukaci cimma yarjejeniyar hada kan kasa

Shugabar Brazil Dilma Rousseff da ke fuskantar barazanar tsigewa, ta bukaci a cimma babbar yarjejeniyar hada kan kasa tare da sauya yanayin yadda ake gudanar da siyasa.

Shugabanr kasar Brazil Dilma Rousseff
Shugabanr kasar Brazil Dilma Rousseff REUTERS/Mike Segar
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan jaridar Folha de Sao Paulo ta fitar da rahoton da ke cewa, an yi amfani da kudaden haramun a yakin neman zaben Rousseff a shekarar 2014.

Jaridar ta rawito Otavio Marquez Azevado, tsohon shugaban kwamintin gudanarwa na kamfanin gine –gine na Andrade Gutierrez na bayar da sheda a gaban masu shigar da karar da ke bincike kan badakalar Petrobras

Otavio ya ce, miliyoyion dalar amurka da aka zuba a asusun yakin neman zaben Rousseff a shekarar 2014, an same su ne ta haramtacciyar hanya, domin kuwa kudadden rashawa ne masu nasaba da kwantirgain da aka bai wa tsohon kamfaninsa nasa.

To sai dai rahoton na Folha de Sao Paulo ya ce, har yanzu an gaza gano ko an biya kudaden harum din ne a asusun kwaminitin yakin neman zaben ko kuma a asusun jam’iyyyar Workers Party.

A halin yanzu dai kotun kula da sha’anin zabe na tuhumar Rousseff a asirce akan zargin daukan nauyin yakin neman zabenta da kudaden da aka sato daga kamfanin Petrobras.

Matukar dai kotun ta same ta da laifi, to babu shakka za ta soke nasarar da ta samu a zaben, abinda ke nufin cewa, Roussef da mataimakinta za su yi hannun riga da kujerunsu, sannan kuma a sake gudanar da wani zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.