Isa ga babban shafi
Syria

‘Yan adawar Syria na son a dakatar da tattaunawar Geneva

Masu adawa da shugaban Syria Bashar Assad za su bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da tattaunawar sulhun da ke gudana yanzu haka a birnin Geneva, saboda a cewarsu bangaren gwamnati ba ya fatan ganin tattaunawar ta yi nasara.

Zauren tattauna sasanta rikicin Syria a Geneva
Zauren tattauna sasanta rikicin Syria a Geneva REUTERS/Salvatore Di Nolfi/Pool
Talla

‘Yan adawar sun yi zargin cewa gwamnatin Damascus, na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta a daidai lokacin da ake kan tattaunawar, abin da ke nuni da cewa gwamnati ba ta goyon bayan shirin samar da zaman lafiya karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya.

Rahotanni sun ce daya daga cikin shugabannin ‘Yan adawar ya tuntubi mai shiga tsakanin rikicin kasar Staffan de Mistura da bukatar ganin an dakatar da tattaunawar.

Tun a ranar 13 ga watan Afrilu ne aka soma tattaunawar da nufin kawo karshen rikicin Syria da aka shafe shekaru biyar ana zubar da jinni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.