Isa ga babban shafi
Brazil

Rousseff za ta yaki yunkurin tsige ta

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff da ke cikin tsaka mai wuya ta lashi takobin yaki da yunkurin tsige ta daga karagar mulki yayin da majalisar dattawan kasar ke shirn fara tuhumar ta.

Uwargida  Dilma Rousseff Shugabar kasar Brazil
Uwargida Dilma Rousseff Shugabar kasar Brazil REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Rousseff mai shekaru 68 ta mayar da martani cikin fushi a bainal jama’an bayan majalisar wakilai ta amince da shirin tsigewar a ranar Lahadin da ta gabata.

A jawaban da ta gabatar kai tsaye ta kafar talabijin , uwargida Rousseff ta ce, ranta ya baci game da kudirin tsige ta sannan ta ce, tana da karfi da kuzarin da za ta iya amfani da su domin yaki da kudirin.

Ana dai zargin shugabar da sauya alkaluma a kasafin kudin kasar ba bisa ka’ida, lamarin da ya haddasa cece kucen siyasa a Brazil har ya kai ga wannan mataki na kokarin tsige ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.