Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya bayyana manufofinsa ga Amurka

Mutumin da ke gaba wajen ganin jam’iyyar Republican ta ba shi tikitin takarar shugabancin kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana manufofinsa na kasashen waje idan ya lashe zaben shugaban kasar, inda yake cewa dakile yaduwar tsagerun da ke amfani da addinin Islama shi ne zai sa a gaba.

Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican
Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican REUTERS/Jim Bourg
Talla

Yayin da yake gabatar da manufofin da zai sa a gaba idan ya lashe zaben watan Nuwamba,Trump ya ce dakile yaduwar tsagerun da ke amfani da sunan addinin Islama shi ne zai zama babban abinda Amurka za ta sa a gaba.

Trump wanda ya yi kaurin suna kan matsayinsa na karbar baki musaman 'yan kasar Mexico da kuma Musulmi a Amurka ya ce, ya zama dole ga kasashen da ke kawance da Amurka su biya ta kudade don kare su daga wata barazana ko kuma su kare kan su.

Dan takarar wanda ya bayyana manufofin kasashen waje na shugaba Barack Obama a matsayin abin takaici ya ce, manufarsa za ta zama wadda za ta sanya Amurka a gaba fiye da kowace kasa, inda ya ce, zai bukaci kawayen kasar su bada gudunmawar kudade domin samar da tsaro a duniya.

Dangane da kasuwanci Trump ya ce, ya zama wajibi su zauna da China don sake duba kasuwanci a tsakanin su da kuma hana kasar karya darajar kudinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.