Isa ga babban shafi
Syria

Amurka da Rasha za su magance rikicin Syria

Kasashen Rasha da Amurka sun amince su ci gaba da kokari wajen samo hanyar magance rikicin Syria da yaki ya daidaita da kuma tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a fadin kasar.

Shugaban Rasha, Vladmir Putin da Barack Obama na Amurka
Shugaban Rasha, Vladmir Putin da Barack Obama na Amurka REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Gwamnatin Bashar Al assad da ke samun tallafin kasar Rasha ta ki daraja yarjejeniyar, abinda ya kai dakarun gwamnati yi wa 'yan tawaye ruwan wuta musaman a yankin Aleppo, inda a 'yan kwanakin nan kusan mutane 300 suka hallaka, cikin su kuwa har da marasa lafiya da ke kwance gadon asibiti.

Samar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta baiwa al'ummar da sojojin suka yi wa kawanya damar samun sukuni bayan sun shiga tsaka mai wuya sakamakon lugudan wutar da dakarun gwamnati ke yi.

A ranar Litinin cikin dare aka kara wa’adin dokar tsagaita wuta a yankin Aleppo da kwanaki biyu bayan la’akari da yawan al’ummar da suka rasa rayukansu a yankin da kuma samun damar fadada aikin jinkai ga daukacin masu bukata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.