Isa ga babban shafi
Britaniya

Za a fallasa wadanda suka boye kaddarori a Britaniya

A jawabinsa da ya gabatar a zauren taron yaki da rashawa a birnin London, firaministan Birtaniya David Cameron ya ce za a bude wani zaure na tattauna yadda za a dawo wa kasashe kadarorinsu da wasu suka sace suka boye a wasu kasashe. 

Friministan Britaniya David Cameron
Friministan Britaniya David Cameron REUTERS/Leon Neal/Pool
Talla

Cameron ya ce zauren zai kunshi hukumomin yaki da rashawa na gwamnatocin kasashe.

A badi ne za a fara bude zauren tattaunawar a Amurka, tare da jagorancin Birtaniya da Bankin duniya da kuma Majalisar dinkin duniya.

Sannan mataki na farko da zauren zai fara mayar da hankali shi ne yadda za a dawo wa kasashe irinsu Najeriya da Tunisia da Ukraine da kuma Sri Lanka kudadensu da a aka boye a wasu kasashe.

Sannan Firaministan ya ce yanzu wajibi ne ga kamfanonin kasasheb waje dake Birtaniya su bayyana kadarorinsu a kundin rijistar da aka tanadar.

Haka ma a taron na yaki da rashawa, kasashen Najeriya da Afghanistan wadanda Firaministan Birtaniya ya ce rashawa ta mamaye kasashen sun ce zasu samar da sabuwar rijistar ta bayyana kadarorin kamfanoni da ke aiki a kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.