Isa ga babban shafi
Amurka

Dan IS ne ya harbe mutane 50 a Amurka

Shugabannin Kasashen duniya tare da Fafaroma Francis da fitattun shugabanin Musulmin Amurka sun la’anci kazamin harin da wani matashi wanda ya yi mubaya’a ga kungiyar IS ya kai a Orlando tare da kashe mutane 50 da jikkata wasu da dama.

Omar Mateen wanda ya harbe mutane 50 a Amurka
Omar Mateen wanda ya harbe mutane 50 a Amurka
Talla

Shugaba Barack Obama ya bayyana harin a matsayin ta’addanci inda ya bukaci sauke tutar kasar yau a fadin duniya, tare da soke shirin fara yakin neman zaben da zai yi wa Hillary Clinton yar takarar Jam’iyyar Democrat a zaben shugaban kasa.

Hukumar bincike ta FBI ta ce Wani matashi dan shekaru 29 Ba’amurke mai suna Omar Mateen amma dan asalin Afghanistan ne ya bude wuta kan mai uwa da wabi a gidan cashewar na ‘Yan luwadi da Madigo.

Yanzu haka kuma kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a duniya ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin.

Akalla mutane 50 Mateen ya bindige tare da jikkata wasu da dama bayan ta bude wuta a wani gidan cashew na ‘yan luwadi da ke birnin Orlando na jihar Florida a Amurka.

01:30

Rahoton Yakubu Lukman daga Florida

RFI

Wannan ne dai hari mafi muni da aka taba gani a Amurka tun bayan harin 9/11 a New York.

Wadanda suka tsira a lamarin sun kwatanta yadda dan bindigan mai suna Omar Mateen ya yi amfani da harsasai wajen yin kaca-kaca da gidan rawan da ‘yan Luwadin ke taruwa duk dare domin holewa.

Wani jami’n hukumar leken asirin kasar, Ronald Hopper ya tabbatar da cewa dan bindigar ya rasa ransa a arangamar da ya yi da ‘yan sanda bayan ya yi garkuwa da su a gidan rawan.

Bayan harin Orlando a Florida, ‘Yan Sanda a California da ke sun kama wani matashi mai suna James Howell da ya shirya kai hari kan ‘Yan luwadi da madigo da ke shirin jerin gwano a Los Angeles.

‘Yan Sandan sun ce an kama Howell ne kusa da Santa Monica dauke da makamai da kuma albarusai da sinadarin hada bam a cikin motar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.