Yau ne ranar kare zabaya ta duniya
Yau ne ranar fafutukar kare zabaya ta duniya da Majalisar dinkin duniya ta ware domin fadakarwa da kuma kokarin kawo sauyi a zamansu a kasashen kudancin Afrika.
Wallafawa ranar:
Azabtarwa da muzgunawa da kisa na daga cikin matsallolin da zabaya ke fuskanta a wasu kasashen duniya.
Shekara daya kenan da Majalisar dinkin duniya ta samar da wannan ranar ta kare zabaya daga fuskantar musgunawa musaman a kasashen kudancin sahara da kasashen da suka hada da Tanzania da Jamhuriyar demokradiya Congo da Burundi da Malawi da kuma Cote d’ivoire.
Babbar jami’ar hukumar kare hakkokin bil Adama da kuma kare zabaya a duniya, Ikponwosa Ero, wadda ita ma zabaya ce kuma 'yar asalin Najeriya ta sanar da wani sakamakon bicinke da ke nuna yadda ake a muzugunawa mutanen da ke da wannan lalura.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu