Isa ga babban shafi
Afghanistan

Kungiyar Taliban Ta Kashe 'Yan Sanda 30 a kasar Afghanistan

Kungiyar Taliban ta kashe akalla ‘Yan sanda 30  tare da raunana sama da 58 a wani harin bom da ta kai wa tawagar motocin da ke dauke da ‘Yan sanda a Kabul na kasar Afghanistan.

Jamian tsaro a Afghanistan suna duba wata mota  da aka wata mota da aka kai mata harin bam ranar 20 ga wannan wata.
Jamian tsaro a Afghanistan suna duba wata mota da aka wata mota da aka kai mata harin bam ranar 20 ga wannan wata. Reuters/路透社
Talla

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya bayyana harin da cewa laifin cin amanan biladama ne.

Wannan hari na zuwa ne mako daya bayan kashe wasu jami'an tsaro 14 dake kan hanyar su ta zuwa aiki a ofishin jakadancin kasar Canada.

Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce 'yan sandan na cikin jerin gwano na motocin su ne a yankin Kabul aka kai masu hari yau Alhamis.

Ganau sunce daya daga cikin maharan na tafe ne a kasa, yayin da wani ke cikin wata mota da aka shake ta  da bama-bamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.