Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton ta Amurka ta tsallake rijiya a FBI

Hukumar bincike ta Amurka ta ce ba za ta bayar da umarnin tuhumar Hillary Cliton ba kan yadda ta yi amfani da kafar sadarwa ta email mallakinta wajen gudanar da harkokoin gwamnatin kasar a lokacin da ta ke rike da mukamin sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Hilary Clinton tare da shugaban Amurka Barack Obama
Hilary Clinton tare da shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Brian Snyder
Talla

Sai dai Darektan hukumar ta FBI, James Comey ya bayyana Mrs. Clinton a matsayin wadda ta yi sakaci wajen kula da wasu bayanan sirri.

Wannan dai wata gagarumar nasara ce ga Clinton dangane da fafutukar ta neman tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar Democrat.

Sai dai bisa dukkan alamu wannan matakin bai yi wa Donald Trump na Republican dadi ba.
 

A bangare guda, Shugaban Amurka Barack Obama ya taya Hillary Clinton yakin neman zabe a jihar North Carolina, inda ya fada wa dandazon jama’a cewa, a shirye yake ya mika wa Clinton ragamar jagorancin kasar.

Shugaban ya ce, babu wani dan takara da ya kintsa domin maye gurbinsa kamar Mrs. Clinton wadda ta kalubalaci Obama wajen neman tikitin takara a shekara ta 2008.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.