Isa ga babban shafi
Birtaniya

Yau Theresa May ke karbar ragamar Birtaniya

Yau ake saran Theresa May za ta karbi ragamar jagorancin Birtaniya a matsayin firaminista kasar sakamakon murabus din David Cameron bayan shan kaye a zaben raba gardama.

Sabuwar firaministar Birtaniya Theresa May
Sabuwar firaministar Birtaniya Theresa May
Talla

Jiya kafofin yada labaran Birtaniya sun dauko hotunan Cameron na kwashe kayansa daga gidan firaministan da ke lamba 10 a Downing Street.

Theresa May ta kasance mace ta biyu da za ta rike wannan mukami a Britaniya tun bayan Margaret Thatcher kuma ta samu wannan matsayin ne sakamakon murabus din  Cameron wanda ya kasa samun hadinkan al’ummar kasar wajen ci gaba da zama a tarayyar Turai.

May mai shekaru 59 a duniya, ma'abociyar wasannin cricket ce yayin da ta karanci ilimin yanayi a jami’ar Oxford tsakanin 1977-83, inda a can ta hadu da mijinta ma’aikacin banki Philip wanda aka kashe ba tare da sun samu haihuwa ba.

May ta yi aiki a ma’aikatun kudade da dama, ya hada da Bankin Ingila kafin a zabe a matsayin ‘yan majalisa a shekarar 1997 mai wakiltan Maidenhead

A shekarar 2002-2003 May ta kasasnce shugabar jam’iyyar Conservative kuma tun a shekarar 2012 ta ke rike da mukamin sakariyar cikin gida da kuma ma’aikatar mata da dai-daito, ta kasance wacce ta fi jimawa kan wannan mukami tun bayan Jaes Chuter Ede shekaru 60 da suka gabata.

May dai ba ita kadai ta nemi wannan kujera ba, sai dai abokiyar takararta Andrea Leadsom ta janye daga takarar neman kujerar firaminista, lamarin daya bai wa May nasara.

Yanzu haka dai akwai kalubale da dama a gaban Theresa May, musamman yadda ake jiran matsayinta kan huldar kasar da kasashen Turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.