Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya dauki Mike Pence mataimaki

Wasu majiyoyi daga Jam’iyyar Republican sun ce Dan takarar shugabancin kasa a Jam’iyyar Donald Trump ya sanar da su kan daukar Gwamnan Jihar Indiana Mike Pence a matsayin dan takarar mataimakinsa.

Dan takarar shugaban kasar Amurka a Jam'iyyar Republican Donald Trump tare da Gwamnan Indiana Mike Pence
Dan takarar shugaban kasar Amurka a Jam'iyyar Republican Donald Trump tare da Gwamnan Indiana Mike Pence REUTERS
Talla

Tuni dai Kafofin yada labaran Amurka suka ruwaito cewar Gwamna Jihar Indiana Mike Pence ake sa ran Trump zai dauka a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

A ranar Juma’a Dan takarar na Republican Donald Trump zai sanar da mataimakinsa a Manhattan. Amma majiyoyi daga Jam’iyyarsa ta republican sun ruwaito cewa dan takarar ya shaidawa ‘Yan Jam’iyyar cewa ya zabi Pence.

Kodayake ana tunanin zai iya sauya tunani akan zabin Mike Pence.

Akwai Gwamnan Jihar New Jersey Chris Christle da ake hasashen Trump zai dauka matsayin mataimaki ko kuma gogaggen dan siyasa Newt Gingrich wanda ya taba zama kakakin Majalisa a zamanin mulkin Bill Clinton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.