Isa ga babban shafi
Syria

'Yan tawayen Syria sun kai gagarumin farmaki a Aleppo

'Yan tawayen Syria sun kaddamar da gagarumin farmaki kan dakarun gwamnatin kasar da nufin karbe wasu yankunan birnin Aleppo da dakarun ke rike da su.

'Yan tawayen Syria sun kaddamar da gagarumin farmaki a yankunan da dakarun gwamnatin kasar ke rike da su a birnin Aleppo
'Yan tawayen Syria sun kaddamar da gagarumin farmaki a yankunan da dakarun gwamnatin kasar ke rike da su a birnin Aleppo REUTERS/Ammar Abdullah
Talla

Tun a ranar 17 ga watan Yuli ne, dakarun shugaban Syria Bashar al-Assad suka kewaye yankunan Aleppo da ‘yan tawayen ke rike da su.

Dakarun dai sun datse hanyar Castello wadda ita ce, babbar hanyar shigar da kayayyaki ga ‘yan tawayen a Aleppo.

A cikin sanarwar da suka fitar, kungiyoyin mayakan da suka hada da Ahrar al- Sham da Jabhat Fateh al- Sham sun ce, sun fara yaki don ganin sun sake bude wata sabuwar hanyar isar musu da kayayyaki.

Kungiyar Fateh al Sham dai ita ce, ta kaddamar da hare-haren bama-bamai kan dakarun gwamnatin da ke aiki a yankin Suburban Rashidin wanda ke kudu maso yammacin Aleppo.

Kananan yara uku na cikin mutane 11 da suka rasa rayukansu a hare-haren rokan da ‘yan tawayen suka harba daga Rashidin zuwa Hamdaniyeh da ke yankin yammacin birnin, inda wasu dakarun gwamnatin ke rike da shi.

An kaddamar da sauran hare-haren ne a Ramussa da ke kudancin Aleppo.

Kungiyar da ke sa ido kan Syria ta ce, za a dauki tsawon lokaci ana gwabza yaki mai zafi tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.