Isa ga babban shafi
Amurka

Daular Larabawa ta karbi fursunonin Guantanamo 15

Kasar Daular Larabawa ta karbi fusrononin Amurka 15 daga gidan yarin Guantanamo, wanda shi ne adadi mafi girma a kokarin da gwamnatin Barack Obama ke yi na rufe gidan yarin.

Yanzu adadin fursunoni 61 ne suka rage a gidan yarin Guantanamo
Yanzu adadin fursunoni 61 ne suka rage a gidan yarin Guantanamo REUTERS/Michelle Shephard/Pool/File Photo
Talla

Amurka ta dade tana neman kasar da za ta amince ta karbi fursnonin wadanda ake tsare da su kan laifukan ta’addanci.

Tun harin 11 ga watan Satumba na 2001, kimanin fursunoni 780 Amurka ke tsare da su a gidan yarin na Guantanamo.

Yanzu adadin fursunoni 61 ne suka rage a gidan yarin bayan Daular Larabawa ta karbi 15 a yau Litinin.

Sanarwar da gwamnatin Amurka ta fitar, tace daga cikin fursunonin 15 da aka kai Daular larabawa, 12 daga cikinsu yan kasar Yemen ne, uku kuma ‘yan Afghanistan.

A cikin sanarwar Amurka ta godewa Daular Larabawa na amincewa ta karbi fursunonin wanda ya nuna goyon bayanta ga kokarin gwamnatin Obama na rufe gidan yarin.

Amurka dai ta dade tana neman kasar da za ta amince ta karbi ‘yan kasar Yemen, wadanda ake gwabza fada a kasarsu.

Shugaba Barack Obama ya yi alkawalin rufe gidan yarin na Guantanomo kafin kawo karshen mulkin shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.