Syria
An kashe ministan labaran IS a Syria
Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana cewa, wani harin jiragen sama da aka kai a Syria, ya kashe ministan yada labaran kungiyar IS mai da’awar jihadi.
Wallafawa ranar:
Talla
Mai magana da yawun ma’aikatar Peter Cook ya ce, a ranar 7 ga watan Satumba ne, rundunar hadin gwiwar ta kashe Wa’il Adil Hassan Salman al-Fayad, wanda aka fi sani da Dr. Wa’il a kusa da birnin Raqa.
Dr. Wa’il dai, shi ne mai kula da fayafayen bidiyon farfaganda da kungiyar ke yadawa, in da ta ke nuna yadda take azabtar da mutane da kuma fille kawunansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu