Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Farfesa Habu Muhammad kan Syria

Wallafawa ranar:

A yau Laraba, kasar Rasha ta sanar da shirin gudanar da tattaunawa da Amurka da sauran kasashe masu ruwa da tsaki kan yakin Syria a karshen wannan mako, irinsa na farko tun bayan karya yarjejeniyar bude wuta na wucen-gadi da kasashen suka yi.Tattaunawar da za ta hada da Turkiyya da Saudiya da kuma watakila Qatar, na zuwa ne a dai-dai lokacin da shugaba Erdogan na Turkiyan ke nuna fargaban barkewar gagarumin yaki tsakanin Amurka da Rasha kan Syrian. A zantawarsu da Umaymah Sani Abdulmumin, Farfessa Habu Muhammad, masanin harkokin siyasar duniya da ke jami’ar Bayero ta Kano, yace har yanzu fa, wadanan kasashen basu shirya kawo karshen yakin Syria ba.

Yankin Aleppo na Syria na ci gaba da fuskantar hare-hare da dama
Yankin Aleppo na Syria na ci gaba da fuskantar hare-hare da dama REUTERS/Abdalrhman Ismail
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.