Isa ga babban shafi
Sudan

Amurka ta tsawaita takunkumi akan Sudan

Shugaba Barack Obama ya tsawaita takunkumin da Amurka ta kakabawa Sudan na tsawon shekara guda, saboda yadda manufofin gwamnatin Khartoum ke ci gaba da zama barazana ga tsaron Amurka.

Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir
Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir REUTERS
Talla

Tun a 1997, Amurka ta kakabawa Sudan takunkumi kan zargin goyon bayan kungiyoyin ta’adda, inda Tsohon shugaban Al Qaeda Marigayi Osama Bin Laden ya zauna a Khartoum na tsawon shekaru hudu tsakanin 1992 zuwa 1996.

Sudan na cikin sunayen kasashen da Amurka ta zayyana a matsayin masu taimakawa ‘Yan ta’adda.

A yau Litinin ne kuma Obama ya tsawaita takunkumin na tsawon shekara guda da zai soma aiki daga ranar 3 ga watan Nuwamba.

Sai da kuma a wata sanarwa da ofishin jekadancin Amurka ya fitar ta ce akwai yiyuwar sassauta takunkumin akan Sudan.

Da farko an yi has ashen cewa Amurka na iya sassautawa Sudan takunkumin bayan ziyarar da jekadan kasar na musamman Donald Booth ya kai kwanan baya a Khartoum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.