Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya za ta kwace kadarar masu take hakki

Majalisar Birtaniya ta gabatar da wani kuduri da zai bai wa gwamnatin kasar damar kwace duk wata kadara da ke kasar mallakar wadanda ake zargi da tauye hakkin dan Adam.

Majalisar dokokin Birtaniya
Majalisar dokokin Birtaniya UK Parliament/Jessica Taylor/Handou
Talla

'Yan Majalisar sun dauki wannan matakin ne cikin wani shiri da suka kaddamar domin tunawa da Sergie Magnitsky, wani lauya da ya yi fice wajen gwagawarmaya.

Sergie Magnitsky wanda dan kasar Amurka ne da aka haifa a Birtaniya kuma ya yi aikin Lauya a Rasha, ya yi suna ne a lokacin da ya bankado yadda manyan ma’aikatan gwamnati a Rasha suka yi sama da fadi da kudaden jama’a.

Jim kadan  da aukuwar wannan lamarin ne, aka kama lauyan bisa zargin sa da kin biyan haraji, in da kuma ya gamu da ajalinsa bayan shafe watanni 11 a tsare.

An dai bayyana wannan kuduri ne a jiya Litinin wanda kuma cikin watan Disamba da muke ciki ake sa ran tabka muhawara a kansa a zauren Majalisar ta Birtaniyar.

Matukar aka amince da kudurin, to zai bai wa alkalai damar kwace kadara da kuma dakatar da asusun bankuna na wadanda ake zargi da tauye hakkin dan Adam.

A halin da ake ciki dai, 'yan Majalisar 27 ke goyon bayan dokar da za ta amsa sunan Magnitsky Amendment a Turance, wadda hatta Amurka ke amfani da ita wajen kwace kadarorin manyan jami’an Rasha da ke da hannu wajen mutuwar lauya Magnitsky.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.