An kaddamar da gidauniyar taimaka wa Sahel
Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar Dala biliyan kusan 3 don taimaka wa mutanen kasashen da ke yankin Sahel da rikicin Boko Haram ya shafa, abin da ya jefa su cikin mawuyacin hali.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Majalisar ke cewa, talauci da yunwa da gurbacewar yanayi zai shafi mutane akalla miliyan 15 a wannan yankin.
Ofishin da ke kula da ayyukan agajin gaggawa na Majalisar ya ce, kashi 40 cikin 100 na kudaden za a yi amfani da su ne wajen tallafa wa mutane miliyan 7 da rikicin Boko Haram ya shafa a arewa maso gabashin Najeriya.
Wata kididdiga ta nuna cewa, akalla mutun guda daga cikin mutane shida a yankin Sahel na fama da yunwa, yayin da kuma kananan yara da dama ba sa samun wadataccen abinci mai gina jiki a yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, karuwar mutanen da ke tsere wa gidajensu saboda tashin hankali a yankin Sahel, ta tsananta matsalar kwararar 'yan gudun hijira a Turai da kuma shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Masu bukatar agaji a Afrika za su karu, matukar adadin yawan al'ummar nahiyar ya kai sama da biliyan 2 nan da shekarar 2050, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu