Isa ga babban shafi
Syria

Fararen hula za su fara ficewa daga Aleppo

Raha da Turkiya da ‘yan tawayen Syria sun kulla wata yarjejeniya ta wasu sa’oi da za ta bai wa farare damar ficewa daga Aleppo sakamakon matsin lamba daga sassan duniya. 

Fararen hula na cikin tsaka mai wuya a Aleppo
Fararen hula na cikin tsaka mai wuya a Aleppo
Talla

Bangarorin uku duk sun tabbatar da yarjejeniyar wadda ake kallon ta a matsayin wata gagarumar nasara ga shugaba Bashar al Assad, wanda ya kwashe shekaru 5 yana fafatawa da masu neman ganin bayansa.

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin ya ce, yau da safe ake saran fara kwashe fararen hular.

Kasar Amurka ta bayyana cewa, ba a tuntube ta ba kan wannan yarjejeniyar, amma ta yi marhaba da duk wani shiri da zai tabbatar da lafiyar fararen hula a Aleppo.

Yarjejeniyar na zuwa ne bayan Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ta samu rahoton da ke cewa, dakarun gwamnatin Syria sun hallaka fararen hula 82 da suka hada da kananan yara da mata a 'ya kwanakin nan a Aleppo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.