Isa ga babban shafi
Isra'ila-MDD

Isra’ila ta kira Jekadanta na Amurka

Isra’ila ta nuna bacin ranta ga kasashen duniya da suka jefa kuri’ar amincewa da wani kuduri da ke neman kasar ta dakatar da gina sabbin gidaje a yankunan Falasdinawa da ta ke ci gaba da mamayewa.

Benjamin Netanyahu Firaministan Isra'ila
Benjamin Netanyahu Firaministan Isra'ila REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Isra’ila ta kira jekadanta na Amurka bayan kasar ta kauracewa kuri’ar da aka kada a zauren kwamitin sulhu wanda ya nuna Amurka tana goyon bayan kudirin.

Wannan na zuwa bayan Ma’aikatar wajen Isra’ila ta gayyaci jakadojita na kasashe 10 daga cikin14 da suka jefa kuri’ar amincewa da kudurin na dakatar da ita daga ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawa.

Isra’ila dai ta yi haka ne domin nuna rashin jin dadinta da kudurin, kuma a cewar Firaminista Benyamin Netanyahu, Isra’ila za ta dauki mataki.

A ranar Juma’a ne kwmitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da matakin yin allawadai da mamayar da Isra’ila ke yi wa yankunan Falasdinawa wanda shi ne karon farko tun 1979.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.