Isa ga babban shafi
Isra'ila

Kotu ta samu Azaria da laifin kashe Bafalasdine

Kotun sojin Isra'ila ta samu wani sojan kasar da laifin kisan kai ta hanyar harbe wani Bafalasdine da ba ya dauke da makami har hahira a birnin Hebron da ke Yamma ga kogin Jordan.

Elor Azaria da ake tuhuma da kisan wani matashin Bafalasdine a Isra'ila
Elor Azaria da ake tuhuma da kisan wani matashin Bafalasdine a Isra'ila Jack Guez/AFP/Getty Images
Talla

Kotun ta samu Elor Azaria da laifin kashe Abdul Fatah al-Sharif mai shekaru 21 a dai dai lokacin da marigayin ke tsare a karkashin ikon jami'an tsaro bayan sun kama shi saboda da harin wuka da ya kai wa wani sojan Isra'ila a cikin watan Maris.

Tuhumar Azaria ta haifar da ra’ayoyi maban-banta a Isra’ila, in da wasu ke ganin ya dace a hukunta shi saboda karya dokar soji, yayin da wasu ke ganin cewa, abin da ya aikata daidai ne.

Azaria ya kashe al-Sahrif ne a yayin da Falasdinawa suka zafafa hare-haren wuka kan yahudawa a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.