Isa ga babban shafi
Iran

Ambaliyar Ruwan Sama Ta kashe Mutane 35 a kasar Iran

A kasar Iran,  mutane 35 suka gamu da ajalinsu sakamakon ambaliyar ruwan sama, yayinda wasu mutanen  takwas har yanzu ba’a san inda suka makale ba.

Shugaban Iran Hassan Rohani a wani hoto da aka dauka ba da dadewa ba
Shugaban Iran Hassan Rohani a wani hoto da aka dauka ba da dadewa ba © Reuters
Talla

Kafofin yada labarai dake kasar musamman gidajen Talabijin sunyi ta nuna hotunan barnar da ambaliyar ruwan ta yi.

Bayanai na cewa an sami ambaliyan ruwan saman  a dukkan yankuna na kasar.

Rahotanni na nuna tun jiya Juma'a ake shatata ruwan sama a wasu sassan kasar da fasa kananan kwalbatoci da mamaye hanyoyi da gidaje da tafiya da motoci da aka ajiye a gefen hanya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.