Isa ga babban shafi
Venezuela

Maduro ya yi karin albashin ma’aikata a Venezuela

Yayin da yau ake cika wata guda da fara zanga zangar adawa da Gwamnatin shugaba Nicolas Maduro na Venezuela wanda ya kai ga kashe mutane 28 yanzu haka, shugaban kasar ya bada umurnin kara albashin ma’aikata da ya kai kashi 60 na abin da suke karba yanzu.

An shafe watanni ana zanga-zangar kyamar gwamnatin Maduro a Venezuela
An shafe watanni ana zanga-zangar kyamar gwamnatin Maduro a Venezuela Reuters
Talla

Karin wani yunkuri ne na kwantar da hankalin wasu daga cikin masu zanga zangar da ke neman ganin bayan shugaban.

Bayan Karin albashin Shugaba Maduro ya kuma bada umarni sassauta farashin kayyakin abinci, domin samawar ma’aikata da sojin kasar sauki.

Venezuela ta shafe tsawon watanni babu zaman lafiya. Kuma matsalar ta fi kamari tun barkewar boren matsin tattalin arziki a ranar 1 ga Afrilu wanda ya rikidi ya koma rikici tsakanin masu boren da ‘yan sanda wanda ya janyo hasarar rayukan mutane 28

Masu sa’ido kan kasar sun bayyana fargaban barkewar sabuwar tarzoma a yau a ranar ma’aikata, bayan shirya fitowa da ‘yan adawa suka yi.

Shugaban Mabiya Katolika Fafaroma Francis, ya sha tayin shiga tsakanin gwamnatin Maduro da ‘yan adawa, wanda a lokuta da dama bangarorin ke hawan kujeran naki.

Sai dai ana sa ran sabon matakin Karin albashi da Maduro ya yi a yau zai kawo karshen rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.