Isa ga babban shafi
Syria

'Yan gudun hijirar Syria sun koma gida

Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, kusan mutane dubu 500 da yakin Syria ya raba da muhallansu, sun koma gida don sanin halin da iyalansu ko kuma kadarorinsu ke ciki.

'Yan gudun hijirar Syria sun koma gida don sanin halin da iyalansu da kadarorinsu ke ciki
'Yan gudun hijirar Syria sun koma gida don sanin halin da iyalansu da kadarorinsu ke ciki Khalil MAZRAAWI / afp
Talla

Hukumar ta ce, tun daga watan Janairun da ya gabata, kimanin mutane dubu 440 da suka rasa matsugunnansu a kasar suka koma gida musamman mazauna yankunan Aleppo da Hama da Homs da Damascus kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Andrej Mahecic ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva.

Mahecic ya ce, an kuma samu wasu ‘yan gudun hijirar daban da ke samun mafaka a kasashe makwabta da suma suka koma Syria kuma adadinsu ya kai dubu 31.

A halin yanzu dai, adadin ‘yan gudun hijirar kasar da suka dawo daga kasashe makwabta tun daga shekarar 2015, ya kai dubu 260.

Sai dai wadannan alkaluma ba su taka kara sun karya ba, idan aka yi la’akari da jumullar mutanen Syria miliyan biyar da ke samun mafaka a wasu kasashen yankin Asiya.

A bangare guda, Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Staffen de Mistura ya shaida wa kwamitin sulhu cewa, an samu sassauncin rikici a kasar tun bayan yarjejeniyar da aka kulla a ranar 4 ga watan Mayun da ya gabata, abin da ya sa daruruwar jama’a ke ci gaba da tsira da rayukansu a ko wani mako.

Rikicin Syria dai ya lakume rayukan mutane fiye da dubu 300 a cikin shekaru shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.