Isa ga babban shafi

Hukumar 'yan sanda ta kame gurbatattun magunguna na dala miliyan 51

Hukumar ‘yan sandan duniya ta INTERPOL, ta sanar da kwace kwayoyi da magunguna marasa inganci da kudin su ya zarce Dala miliyan 51, a samamen da ta kaddamar cikin mako guda.

Wasu jami'an hukumar 'yan sanda ta duniya INTERPOL, yayinda suke atasaye a birnin Beijing na kasar China.
Wasu jami'an hukumar 'yan sanda ta duniya INTERPOL, yayinda suke atasaye a birnin Beijing na kasar China. REUTERS/Stringer/File Photo
Talla

Hukumar dake da cibiya a birnin Lyon, tace magungunan sun hada da na rage zafin cuta, ciwon ido, da kuma na ciwon farfadiya.

Hukumar tace tayi aikin ne, tare da jami’an Kwastam da jami’an kula da lafiya a kasashe 123, kuma yanzu haka ta kama mutane sama da 400.

Sanarwar hukumar ya nuna cewa wannan shi ne karo na farko da kasashen Afirka suka shiga cikin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.