Isa ga babban shafi
Italiya

Kallon bidiyon batsa na rage kaifin basira ga matasa

Masana kiwon lafiyar kwakwalwa sun yi gargadin cewa kallon hotuna da bidiyon batsa a Intanet na canza kwayar halittun kwakwalwar mutane musamman ma yara da suka balaga.

Kallon Hutunan Batsa na barazana ga lafiyar kwakwalwar yara
Kallon Hutunan Batsa na barazana ga lafiyar kwakwalwar yara AFP PHOTO/ Manjunath KIRAN
Talla

Masanan sun fadi haka ne a wani babban taron duniya da aka kammala a Rome a kan hatsarin batsa da yara ke fuskanta a duniyar Intanet.

Donald Hilton wani babban likitan kwakwalwa a Amurka ya yi gargadi kan mummunan tasirin da bidiyon batsa a intanet ke yi a kwakwalwar yara.

Shugaban darikar Katolika Fafaroma Francis ne ya jagoranci taron na masana sama da 150 a fannin kimiya da ilimi da al’adu da kuma kare hakkin yara kanana da aka kammala a yau Juma'a.

A wajen taron masana sun yi nazari tare da tattauna illar kallon bidiyon batsa a kwakwalwar yara.

Masana sun ce halayyar kwakwalwa na canzawa a yayin da take nazari ko karatu, kuma yakan zama illa idan aka takura kwakwalwa.

An bayyana cewa matasa na shafe lokaci suna kallon bidiyon batsa domin kokarin gamsar da kansu ta hanyar wasa da al’auransu da hannu a yayin da suke kallon bidiyon na batsa.

Taron ya yi kira ga iyaye su farga su lura wajen daukar matakan kula da dabi’un ‘ya'yansu tare da yin kira ga mahukunta su karfafa dokokin kare kananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.