Isa ga babban shafi
Amurka

An yi gwanjon zanen Yesu akan Dala miliyan 450

An yi gwanjon zanen surar Yesu Al-Masihu da Leonardo Da Vinci ya kirkira shekaru 500 da suka gabata akan farashin Dala miliyan 450.3 a birnin New York na Amurka. Wannan dai shi ne farashin gwanjo mafi tsada a bangaren fasahar zane a duniya.

Zanen Salvator Mundi a dakin gwanjo na Christie da ke birnin New York na Amurka
Zanen Salvator Mundi a dakin gwanjo na Christie da ke birnin New York na Amurka Fuente : REUTERS
Talla

farahin gwanjon zanen surar Yesu Al-Masihun da aka yi wa lakabi da Salvator Mundi, wato mai ceton duniya, ya ninka tayin farko na Dala miliyan 179.4 a shekarar 2015.

Jim kadan da sanar da sabon farashin Dala miliyan 450.3 da aka sallama zanen, mutanen da suka yi dandazo a dakin gwanjo na Christie a birnin New York suka barke da shewa.

An fara tayin zanen ne daga Dala miliyan 100 zuwa Dala milyan 400 kafin daga bisani a ka samu wani mutum da ya kira ta wayar tarho, in da ya taya zanen akan Dala miliyan 450.3.

Sai dai ba a bayyana wannan mutumin ba da ya amince ya lale zunzurutun kudin.

Zanen ya nuna Yesu al-Masihu ya daga hannunsa guda, yayin da dayan hannun ke rike da kwallon kwalba da ke nuna taswiyar duniya.

Leonardo Da Vinci da ya zana surar a shekarar 1519, wato kimanin shekaru 500 da suka shude, na da wasu zanen da ba su gaza 20 ba da kuma har yanzu ke ci gaba da wanzuwa.

Ana zaton cewa, zanen na Salvator Mundi, shi kadai ne da har yanzu ke karkashin kulawar wasu mutane daban da ba su da alaka da hukuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.