Isa ga babban shafi
Bangladesh-Myanmar

Myanmar na dab da maido da Musulman Rohingya

Yau ake saran gwamatin Myanmar za ta rattaba hannun kan wata yarjejeniyar maido da dubban Musulman Rohingya da suka tsere zuwa Bangladesh sakamakon tashin hankalin da ya barke a jiharsu ta Rakhine.

'Yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh
'Yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh REUTERS/Mohammad Ponir Hossain
Talla

Sai dai ana fargabar cewa, akwai yiwuwar manyan Jana-Janar na sojin Myanmar su kawo cikas wajen cimma yarjeniyar da Bangladeh wadda ta tsugunar da ‘yan Rohingyan kimanin dubu 600.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun zargi jami’an sojin Myanmar da yi wa matan Rohingya fyade da kuma aikata miyagun laifuka kamar kisa a lokacin rikicin wanda ya barke tsakanin jami’an tsaro da ‘yan tawayen Rohingya a cikin watan Agustan da ya gabata.

Majalisar Diunkin Duniya ta bayyana kisan Musulman Rohingya a matsayin yunkurin sojojin kasar na share wata al’umma daga doran kasa.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tilleron ya bayyana barazanar sanya takunkumi kan wadanda ke da hannu wajen aikata danyen aikin a jihar Rakhine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.