Amurka Na Tuhumar 'Yan Rasha 13, Da Kamfanoni uku Da Kutse A Zaben 2016
Masu bincike dake kasar Amurka na zargin wasu ‘yan kasar Rasha 13 da wasu kamfanoni na Rasha 3 da hannu dumu-dumu wajen katsalandan cikin zaben Amurka da aka yi shekarar data gabata wato 2016.
Wallafawa ranar:
Ofishin mai bincike na musamman Robert Mueller sun bayyana cewa akwai zagon kasa da aka kulla da nufin mara baya ga yakin neman zabe na dan takaran jam'iyar Republican Donald Trump, bisa ‘yar takara na jam'iyar Democrat Uwargida Hillary Clinton.
Rahoton na zargin cewa tun a shekara ta 2014 aka fara kulle-kullen yin kutse cikin zaben na Amurka kafin ma Donald Trump ya bayyana shirinsa na tsayawa takara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu