Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta yi barin wutar gargadi a Syria

Dakarun sojin Turkiyya sun yi barin wutar gargadi kan mayakan da ke goyon bayan sojin Syria da suka shiga yankin Afrin a yammacin jiya Talata, yankin da ke karkashin ikon 'yan tawayen Kurdawa. 

Lokacin da dakarun Syria ke kai farmaki kan mayakan da ke goyon bayan sojin Syria a Afrin
Lokacin da dakarun Syria ke kai farmaki kan mayakan da ke goyon bayan sojin Syria a Afrin BULENT KILIC / AFP
Talla

Ma’aikatar yada labaran Syria ta tabbatar da cewa daruruwan sojin Syria da 'yan tawayen Kurdawa ne suka isa yankin na Afrin don nuna tirjiya ga matakin shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiyya. Sai dai kuma sun gaza karasawa da akalla nisan kilomita 10 bayan barin wutar gargadin daga Turkiyya.

Kwararuwar dakarun dai ita ce irinta ta farko karkashin jagorancin kungiyar Kurdawan YPG tun bayan 2012 .

Wata sanarwa da kakakin YPG, Nuri Mahmud ya fitar, ta ce kungiyar ce da kanta ta nemi agajin gwamnatin Syria don fatattakar Turkiyya daga yankin na Afrin kuma cikin gaggawa Bashar al Assad ya amsa tare da aikewa da dakaru, sai dai kuma sun gaza shiga yankin na Afrin.

Tun a shekarar 2012 ne Kurdawan da rike da yankin na Afrin bayan gwamnatin Shugaba Bashar al assad ya janye dakarunsa.

Sanarwar Kurdawan ta ce, za su ci gaba da kokari wajen ganin sun tabbatar da yankin a karkashin ikon Syria don ci gaba da zamowar kasar guda daya dunkulalliya tare da fatattakar Turkiyya daga ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.