Isa ga babban shafi
Rasha

Mutane 64 ne suka mutu a wata gobara a Rasha

Akalla gawarwakin mutane 64 ne aka tarkato bayan lafawar gobarar da ta tashi a wani shagon sayar da kayayakin masarufi dake Kemerovo dake cikin yankin Sibéria a kasar Rasha .

Gobarar da ta tashi  a wani shagon sayar da kayayakin masarufi dake Kemerovo
Gobarar da ta tashi a wani shagon sayar da kayayakin masarufi dake Kemerovo REUTERS/Dmitry Saturin
Talla

Kafofin yada labaran Rasha sun ruwaito bayanai daga jami’an kwana kwana cewa yanzu haka mutane da dama ne suka bata bayan tashin gobarar.

Sakamakon yawan mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu yanzu haka sun zarta 60, wannan ya biyo bayan sakamakon farko ne dake cewa 37 aka gano gawarwakinsu a yayin da wasu 70 suka bata wadanda suka hada da kananan yara 40.

Ita dai wannan gobara ta tashi ne da misalin karfe11 ranar lahadi a hawa na uku kuma na karshe a ginin cibiyar kasuwancin dake kan titin Lénine, a tsakkiyar Keme-rovo.

Rasha dai kasa ce da ake yawan fama da tashe tashen gobara, da ke sanadiyar salwantar da rayukan mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.