Gobara ta hallaka Fursunoni 68 a Venezuela
Hukumomin Kasar Venezuela sun ce gobara a wani wurin da yan sanda ke tsare wadanda ake zargi da aikata laifufuka ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 68, yayin da wasu da dama suka jikata lokacin da wasu da ake tsare da su suka yi yunkurin tserewa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Babban mai gabatar da kara, Tarek Williams Saab ya ce sakamakon wannan hadari da aka samu a tashar yan sandar dake Carabobo sun nada masu bincike guda 4 domin binciko abinda ya faru.
Carlos Nieto, shugaban wata kungiyar agaji, ya ce wasu daga cikin mutanen dake wurin sun kone kurmus, yayin da wasu kuma hayaki ne ya kashe su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu