Isa ga babban shafi
Amurka

Facebook ya amsa laifinsa kan gaza killace sirrin al'umma

Shugaban kamfanin sada zumunta na Facebook, Mark Zukerberg ya amince da sakacin da ya tafka wajen gaza killace bayanan sirrin al’umma. Zukerberg a takaddar neman yafiya da ya aikewa Majalisar wakilan Amurka gabanin gurfanar gabanta, ya ce ya amsa dukkanin laifin da ake tuhumarsa.

Shugaba kuma ma'assasin kamfanin sada zumunta na Facebook Mark Zukerberg.
Shugaba kuma ma'assasin kamfanin sada zumunta na Facebook Mark Zukerberg. REUTERS/Stephen Lam
Talla

Kalaman na Zukerberg na zuwa ne sa’o’I kalilan kafin gurfanarsa gaban majalisar dattijan Amurka don yin jawabi kan yadda kamfanin Cambridge Analytica na Birtaniya da ya gudanar da yakin neman zaben shugaban kasar Donald Trump a 2016 ya tatsi bayanan fiye da mutane miliyan 80.

Cikin takaddar tasa, Zukerberg ya ce shi ne ya assasa kamfanin kuma shi ne ke tafiyar da shi a don haka dole ne ya karbi laifin da kamfanin ya yi inda yana mai cewa babban abin da suka sanya a gaba bai wuce sada al’ummar duniya waje guda ba.

A cewar Zukerberg Kamfanin ya samar da wasu sabbin tsare-tsare da za su bai wa masu amfani da shafinsa damar kare bayanansu na sirri cikin sauki, matakin da ya ce zai bayar da cikakkiyar kariya ga duk wani yunkurin kutse.

A cewarsa Sabbin tsare-tasren na yanzu akwai damar sauya bayanan sirri ko kuma goge su kai tsaye daga shafin.

Zukerberg dai zai gurfana gaban zaman majalisar a ranakun Talata da kuma laraba don amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake yi masa bayan fuskanta matsin lamba daga bangarori daban-daban ciki har da kungiyar Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.