Isa ga babban shafi
Saudiya-Faransa

Faransa za ta tallafawa Saudiya wajen gina gidajen kallo

Faransa za ta taimakawa Saudi Arabiya wajen kafa kungiyar magoga goge, tare da gina gidajen Cinema, rawa, da kade kade a kasar, kamar yadda Ministar raya al'adun Faransar Francoise Nyssen, ta sanar, a dai dai lokacin da Saudiyyar ke ci gaba da maraba ga al'adun kasashen yammacin duniya.

Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman tare da Firaministan Faransa Edouard Philippe.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman tare da Firaministan Faransa Edouard Philippe. REUTERS/Charles Platiau
Talla

A wata tattaunawa da ta yi da manema labarai Nyssen ta ce tuni mahukuntan Saudiya suka sanya hannu kan kwangilar tare da katafaren dakin kallon rawa, kida da waka na birnin paris, da ake cewa l'Opéra de Paris, don taimakawa wajen gina makamantan ta a Saudiyyar.

Tuni dai Françoise Nyssen tare da takwaranta na Saudiya Awwad al-Awwad Suka sanarwa manema labarai matakin jim kadan bayan rattaba hannun kan kwantiragin yau litanin a birnin paris.

Yarjejeniyar Kwantiragin na zuwa ne a dai dai lokacin da Yarima Mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman ke ziyara a Faransa a kokarin da ya ke na zamanantar da masarautar kasar da ke bin tafarkin shari'ar musulunci.

A watan Fabrairun da ya gabata ne Saudiyyar mai bin tsauraran matakan shari'ar musulunci, ta bayyana aniyarta na ware Dalar Amurka har biliyan 64 wajen samar da gine ginen gidajen kallon Cinema, kida , rawa da waka a kasar, yayinda a bangare guda kuma ta shirya gina wadannan gidajen rawar da gugar goge a birnin Jeddah,  da ke yammacin kasar ta saudiya kan gabar kogin maliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.