Isa ga babban shafi
Syria

Gutarres ya gargadi kasashen Duniya akan rashin jituwa

Sakataren Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ci gaba da samun rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen Duniya kan kasar Syria, ka iya kara yawan yake yake ne kawai a tsakaninsu.

Sakataren Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakataren Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres © AP Photo/ Khalil Senosi
Talla

Antonio Gutarres ya bukaci kwamitin sulhu na majalisar dinkin Duniya akan ya dauki matakin da ya dace domin magance wannan matsalar a cikin ruwan sanyi

A yayin da kwamitin sulhu na majalisar dinkin Duniya ke gudanar da zamansa kan batun kasar Siriya, a yau Jumu’a, Sakataren na majalisar dinkin Duniya ya ce: “a cikin shekaru 8 da suka gabata, mutanen kasar Syria sun yi ta shan wahala akan wahala, na jaddada cewar babu hanyar magance wannan matsalar ta daukar matakin Soji”

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya gargadi takwaransa na Faransa Emmanuel Macron akan batun kai wa Syria farmaki da ya ce abu ne mai matukar hatsari. Yayi masa wannan gargadin ne a wata zantawa da suka yi ta Wayar Tarho.

Shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin ya ce abu mafi muhimmanci a yanzu shine a kaucewa tafka barna, ta hanyar daukar matakin da ya kira mafi hatsari da kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa na majalisar dinkin Duniya wanda kuma, ba’a san sakamakon da zai haiufar ba.

Dama dai kasar ta Rasha na ta bayyana cewar ‘yan tawayen da kansu ne suka yi amfani da makami mai guba, amma ba Dakarun Sojin gwamnatin Assad ba kamar yanda ake ta bayyanawa.

To sai dai a zantawar tasu ta wayar Tarho shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya gayawa shugaba Vladimir Putin na Rasha cewar a farko shi ya kuduri aniyar samar da matakin tattaunawa ne tsakanin Rasha da kasarsa wato Faransa dangane da wannan batun, domin samar da zaman lafiya a kasar ta Syria.

Shima dai Antonio Guterres ya yi Allah-wadai da abubuwan da ke faruwa a kasar ta Syria. Ya ce: “Na jaddada matsayi na na yin Ahhal-wadai da amfani da makami mai guba daga kowanne bangare na wannan rikici, kuma ta kowane hali, hakika amfani da karfin Soji abin Allah-wadai ne kuma ya saba wa dokokin kasa-da-kasa”

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin Duniyar na ci gaba da tattaunawa akan bukatun na kasar Rasha da ke so a kaucewar kai wannan harin, a yayin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ke ci gaba da yin tsayin gwamin Jaki kwanaki kalilan da ya gayawa Rasha cewar ta shirya domin Makamai masu linzami na zuwa a cikin kwanaki

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.