Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar Nukiliyarta

Iran ta yi barazanar ficewa daga yarjejeniyar Nukiliyar da ta cimma da kasashen duniya a shekarar 2015, matukar Donald Trump ya kammala fitar da Amurka daga yarjejeniyar wadda a yanzu haka ya ke yi mata shakar mutuwa. Haka zalika Iran din ta caccaki kasashen Turai da suka gaza yin katabus kan matakan da Amurkan ke dauka kan yarjejeniyar.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani. REUTERS/Danish Siddiqui/File Photo
Talla

A wata tattaunawarsa da gidan talabijin din kasar Ali Akbar Velayati babban mashawarci kan harkokin kasasshen waje ga shugaban addinin kasar Ayatollahi Ali Khamenei, ya ce Amurka ta na ficewa daga yarjejeniyar su ma za su fice matakin da ke nuna cewa za su daina mutunta ka'idojin da aka cimma kan yarjejeniyar.

A shekarar 2015 ne Iran din ta cimma yarjejeniyar da kasashen Birtaniya China Faransa Jamus da Rasha karkashin jagorancin Amurka lokacin mulkin shugaba Barrack Obama.

Karkashin yarjejeniyar ta 2015, kasashen za su janye takunkuman da a baya suka kakabawa Iran din sakamakon shirin ta na kokarin mallakar makamin Nukiliya.

A ranar 12 ga watan Mayun da mu ke ciki ne ake saran Amurkan za ta kammala ficewa daga yarjejeniyar, matukar ba a samar da gyare-gyaren da ta ke bukata a cikinta ba.

A yau Alhamis ne ministan harkokin wajen Iran din Mohamed Javad Zarif ya aike da wani gargadi cikin sakon bidiyo da harshen ingilishi ga shugaban na Amurka Donald Trump, inda ya ke cewa matukar suka fice daga yarjejeniyar Iran ma za ta sanar da matsayarta kan abin da ta ke ganin ya dace.

Kawo yanzu dai shugaban addinin Iran din Ayatollahi Ali Khamenei ake jira wanda shi ne zai yanke matakin karshe kan takaddamar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.