Isa ga babban shafi
SAUDI-UNESCO

Wasu yankunan Saudi da Oman sun shiga jerin kayakin UNESCO

Hukumar raya ilmi kimiyya al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO ta sanya yankin Al-Ahsa mai dogon tarihi da ke kasar Saudi Arabia da dadadden birnin Qalhat da ke kasar Oman a jerin guraren tarihi na duniya.

Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman. REUTERS/Amir Levy/File Photo
Talla

Matakin na UBESCO na zuwa a dai dai lokacin da hukumomin kasashen ke kokarin karkata akalar tattalin arzikinsu zuwa fannin da ba na man fetur ba, inda galibi su ke tunanin zuba gagarumin jari a bangaren yawon bude ido.

Tun farko biranen na Riyadh da Muscat ne suka mika bukatar hakan ga hukumar ta UNESCO don janyo hankalin dubban masu yawon bude ido.

Guraren tarihin biyu masana sun yi ittifakin sun shafe daruruwan shekaru tun kafin karni na 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.