Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha za ta fara kallon 'yan jarida a matsayin 'yan leken asiri

Majalisar Dokokin Rasha ta gabatar da wani daftarin doka da zai mayar da 'yan jaridun da ke yi wa kamfanonin kasashen waje aiki a matsayin 'yan leken asirin kasa.

Gwamnatin Rasha na shirin amincewa da dokar ayyana 'yan jarida a matsayin 'yan leken asirin kasa.
Gwamnatin Rasha na shirin amincewa da dokar ayyana 'yan jarida a matsayin 'yan leken asirin kasa. REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Wannan ya biyo matakin da bangaren zartarwar kasar ya dauka a bara na sanya wakilan kamfanonin yada labaran kasashen wajen a matsayin 'yan leken asiri.

Mataimakin shugaban Majalisa, Pyotor Tolstoy ya ce, idan aka amince da wannan doka,  za ta tilasta wa 'yan jaridan bayyana in da suke samun kudadensu da kuma yadda suke kashe su.

Ana kallon dokar a matsayin mayar da martani kan Amurka wadda ita ma ta yi irinta domin bayyana 'yan jaridun Rasha a matsayin 'yan leken asirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.