Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Kowanne mutum guda cikin 9 na fama da tsananin yunwa a duniya - rahoto

Wani rahotan Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar matsanancin yanayi na kan gaba wajen haifar da matsalar yunwa a fadin duniya a shekarar da ta gabata, wanda ke gaba wajen jefa rayuwar mata da jarirai da kuma tsoffi cikin mawuyacin hali.

Rahoton na Majalisar ya bukaci samar da gyare-gyaren da zasu kai ga yakar matsalar ta yunwa wadda ta fi tsananta a kasashen Afrika da kuma yankunan da yaki ya daidaita.
Rahoton na Majalisar ya bukaci samar da gyare-gyaren da zasu kai ga yakar matsalar ta yunwa wadda ta fi tsananta a kasashen Afrika da kuma yankunan da yaki ya daidaita. REUTERS/David Lewis
Talla

Rahotan ya ce matsanancin yanayin da ake samu wanda ke haifar da ruwan sama mai yawa da sauyin yanayi, tare da fari da iskar da ke dauke da ruwan sama da kuma ambaliya sun taimaka wajen kara yawan mutanen da basa samun abinci mai gina jiki zuwa miliyan 821 a shekarar da ta gabata.

Rahotan Majalisar da ke bayani kan harkar samar da abinci ya ce alkaluman da aka bayar sun nuna cewar, kowanne mutum guda cikin mutane 9 a duniya na fama da yunwa, adadin da ya zarce miliyan 804 da aka samu a shekarar 2016.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a cikin shekaru 3 da suka gabata, adadin mutanen da ke fama da yunwa na cigaba da karuwa, kamar yadda aka samu a shekaru 10 da suka gabata.

Rahotan ya ce abin takaici shi ne sama da kashi 22 na kananan yaran da shekarunsu bai gaza biyar ba su suka fi shan azabar matsalar unwar wadda ta shafi mutane sama da miliyan 59 daga kasashe 24 na Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.