Isa ga babban shafi
MDD

Cutuka sun kashe yara sama da miliyan 6 a duniya

Wani rahoton hadin gwiwa da Hukumar Lafiya da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar a wannan Talata, ya bayyana cewa yara kanana milyan 6 da dubu 300 ne suka mutu a cikin shekarar da ta gabata sakamakon kamuwa da cututukan da ake iya daukar matakan kaucewa, abin da ke nufin cewa yaro daya ne ke mutuwa a cikin kowadanne kikoki biyar.

Akwai yiwuwar kananan yara miliyan 56 sun mutu nan da shekarar 2030 muddin ba a dauki matakin magance cutukan da ke haddasa mutuwarsu ba, in ji rahoton Majalisar Dinkin Duniya
Akwai yiwuwar kananan yara miliyan 56 sun mutu nan da shekarar 2030 muddin ba a dauki matakin magance cutukan da ke haddasa mutuwarsu ba, in ji rahoton Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Rahoton ya bayyana cewa yara milyan 5 da dubu 400 na wannan adadi sun mutu ne suna da shekarun da ba su wuce biyar ba a duniya, tare da gargadin cewa matukar dai ba a dauki matakan da suka wajaba ba, yawan wadanda za su mutu zai kai milyan 56 kafin shekara ta 2030.

Laurence Chandy, daraktar sashen tara alkalumma a hukumar UNICEF, ta ce tabbas an samu gagarumin ci gaba a kokarin rage rsasuwar yara kanana a duniya tun cikin shekarun 1990, amma duk da haka wasu milyoyi na ci gaba da mutuwa sakamakon matsalolin da za a iya kauce wa.

Laurence ta ce, karancin magunguna, rashin ruwa mai tsafta da rashin wutar lantarki, su ne manyan matsalolin da suka haddasa rasuwar rabin yara ‘yan kasa da shekaru 5 musamman a kasashen Afrika da ke Kudu da Sahara, sai kashi 30 a yankin Kudancin Asiya.

Dr. Princess Nono Simelela, mataimakiyar daraktan Sashen Kula da Iyali a Hukumar Lafiya ta duniya, ta ce rashin ruwa mai tsafta ko abinci mai gina jiki, na haifar da cututuka kamar karancin jini, gudawa da dai sauransu, wadanda su ne manyan dalilai na mutuwar yara a shekarar da ta gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.