Isa ga babban shafi

Kotun duniya ta baiwa Amurka umarnin dagewa Iran takunkumai

Kotun duniya ICJ, ta baiwa Amurka umarnin cire takunkuman karya tattalin arzikin da ta kakabawa Iran dangane da shirinta na nukiliya.

Alkalan Kotun Duniya ICJ dake birnin Heague.
Alkalan Kotun Duniya ICJ dake birnin Heague. RFI/Dyna Seng
Talla

Tuni dai gwamnatin Iran ta yi maraba da hukuncin, wanda ta ce zai kawo karshen kuncin da Amurkan, ke kokarin sake jefa ‘yan kasarta da gangan, ta hanyar fakewa da zargin bogi na cewa duniya na fuskantar barazanar makaman nukiliya daga gareta.

Baki dayan alkalan kotun duniyar ta ICJ da ke Heague, sun ce matakin Amurkan na sake kakabawa Iran takunkuman karya tattalin arzikin ya sabawa yarjejeniyar kulla kasuwanci da kuma diflomasiyya da kasashen biyu suka cimma a shekarar 1955 kafin juyin juya hali a kasar ta Iran.

Daya daga cikin Alkalan kotun duniyar AbdulQawi Ahmed Yusuf, ya ce takunkuman da suka umarci Amurka da dagewa Iran sun shafi magunguna da sauran kayayyakin asibiti, kayan amfanin gona, da kuma kayayyakin gyaran jiragen sama, da kasar ke saidawa ko saye daga kasashen duniya.

A yanzu dai lokaci ne kawai zai fayyace ko hukuncin kotun duniyar zai yi tasiri ko akasin haka, la’akari da cewa a baya Amurkan da Iran sun sha yin watsi da hukunce hukuncenta.

A watan austan da ya gabata, shugaba Donald Trump ya fara kakabawa Iran takunkuman, bayan da a watan Mayu, ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ta 2015, a watan Nuwamba kuma ake sa ran Amurkan za ta sake kakabawa Iran wasu Karin takunkuman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.